Amma duk da haka ra'ayoyin kasashen larabawa suna ganin cewa , ko farmakin da aka yi ya yi tsanani sosai , ba za a hana gudanarwar farfado da kasar Iraq . Kuma ba za a girgiza zuciyar jama'ar kasar Iraq don tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya . Babban zaben da aka yi a kasar ya sami nasara . Wannan ya nuna cewa , zukatan jama'ar kasar Iraq ba su son yaki kuma Suna cike da fatan alheri ga tsaron kasar. Sa'an nan kuma sun bayyana cewa , don kiyaye jama'ar Kasar Iraq sosai kuma da wur-wuri za a farfado da zaman lafiyar kasar , dole nen a nan gaba gwamnatin wucin gadi na kasar Iraq ta yi kokari kwarai da gaske . Da farko dai ya kamata sabuwar gwamnati ta himmantar da musulman Sunni da su shiga cikin gudanarwar zaman lafiya . Na biyu ya kamata ta daidaita huldar dake tsakanin kasar iraq da kasar Syria da kasar Iran da sauran kasashen makwabta . (Ado)
1 2 3
|