A ran 28 ga watan da ya wuce a wata cibiyar binciken likitanci da ke birnin Hilla wanda ya ke da nisan kilomita 100 dake kudancin birnin Bagadaza , hedkwatar kasar Iraq an yi afkuwar kunar bakin wake . Yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 125, kuma mutan fiye da 200 sun sami rauni .
Tashar rediyo mai hoto ta Al-Jazeera ta watsa labari cewa , birnin Hilla hedkwatar Lardin Babil dake tsakiyar kasar Iraq. Wannan wani birni ne da musulamai masu ra'ayin Shi'ir da na Sunni suna zaune tare .
Wannan al'amarin ya afku ne bayan da sojojin kasar Amurka da na Iraq sun shelar da cewa , sun sami babban ci gaba a wajen kai naushi ga dakaru masu dauke da makamai dake yin adawa da Amurka. A wannan rana , gwamnatin wucin gadi ta kasar Iraq ta sanar da cewa , kafin kwanaki 3 , an kama Sabawi Tikriti . 'dan
uwar Saddam , tsohon shugaban kasar a iyakar tsakanin kasar Syria da kasar Iraq . Kafin wannan sojojin Amurka da Iraq sun kama wasu mutane masu ba da taimako ga Abu Musab , babban mutum na 3 na Kungiyar Al-Qaeda . Saboda haka wasu jami'ai na kasar Amurka da Iraq sun yi farin ciki kuma sun kiyasta cewa , a nan gaba kadan halin tsaron kasar Iraq zai kyautatu sosai . Amma haba al'amari mai zubar da jini ya kai bugu mai karfi ga masu rike ra'ayin fara'a kan halin da ake ciki yanzu a kasar Iraq.
1 2 3
|