Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-01 18:13:15    
An sake afkuwar kunar bakin wake a Iraq

cri

A ran 28 ga watan jiya rundunar sojojin kasar Amurka ta bayar da sanarwa cewa , a ran 27 da dare , wani sojan Amurka ya mutu saboda an kai masa farmaki a wata tashar binciken zirga-zirga . Bisa kididdigar da ka yi , an ce, tun daga farkon yakin Iraq a shekarar 2003 , sojojin kasar Amurka na kimanin 1500 sun rasa rayuwarsu a kasar Iraq .

Masu lura da al'amuran duniya sun bayyana cewa , bayan da aka yi babban zabe cikin nasara a kasar Iraq , dakaru masu dauke da makamai dake adawa da Amurka bi da bi ne sun ci gaba da kai farmaki ga sojojin Amurka dake Iraq da 'yan sanda na Kasar Iraq da jimi'an gwamnati da kuma farar hula wadanda suke aiki ga gwamnatin . Wannan don hana gudanarwar farfado da kasar Iraq . Sun kimanta cewa, mai yiyuwa ne a nan gaba kadan dakarun za su kai babban farmaki fiye da da .


1  2  3