|

Kullam gwamnatin kasar Amurka da gwamnatin wucin gadi na kasar Iraki suna son a yi babban zabe a lokacin da aka tsara. Gamnatin kasar Amurka tana tsammani wannan alamar nasara ce ta manufarta a Iraki, gamnatin Allawi tana tsammani ko za a iya yi babban zabe a lokacin da aka tsara ko ba za a iya yi ba wata jarrabawa ce ga karfin yin mulki nata, kuma tana kokarin nema mai da gwamnatin wucin gadi ta zama na doka.
Don tabattar da a yi babban zabe a lokacin da aka tsara, kasar Amurka ta kara sojojinta da ke Iraki, yawansu ya kai dubu 150, kuma ta kara kai farmaki ga 'yan dakaru masu yin adawa da Amurka. Gwamnatin wucin gadi ta kari lokacin halin gaggawa na kasa, ta dauki matakan kara yan sanda da rufe iyakar da ke tsakanin kasar Iraki da Syria don kyautata halin zaman lafiyar kasar. Ban da haka kuma, gwamnatin wucin gadi ta yi ta tabawa da mutanen Sunni wadanda ke kin babban zabe don sa musu canja ra'yoyinsu.
1 2 3
|