Yanzu yin barci a makare ya zama ruwan dare a wajen matasa. Likitocin kasar Sin sun tunatar da matasa da cewa, yin barci ba yadda ya kamata ba, rashin isasshen barci, har ma da yin barci a makare, dukkansu za su sanya jikin dan Adam kasa aiki yadda ya kamata, lamarin da zai yi mummunar illa ga lafiyar dan Adam, wadda ba za a iya zato ba. Don haka dole ne matasa su fito da ajandar hutawa mai dacewa.
Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana bayani da cewa, matsalar barci, wata mummunar alama ce da ke nuna yadda jikin dan Adam ba ya aiki yadda ya kamata. Galibin wadanda suke fama da matsalar barci su kan yi aiki ko wasa da dare, lokacin da wajibi ne a yi barci. Amma a rana kuma, su kan ji barci, lamarin dake haddasa babbar illa ga ayyuka da zaman rayuwa.
Idan wani ya dade bai yi barci yadda ya kamata, to, jikinsa ba ya aiki yadda ya kamata, har ma zai fuskanci matsaloli da dama, alal misali, gazawa wajen mai da hankali kan wani abu, da gazawa wajen yanke hukunci daidai kuma cikin jageren lokaci, da gamuwa da matsalar cin abinci. Idan matasa sun dade ba sa barci yadda ya kamata, ko ba su yi barci isasshe ba, to, za su raunata karfin garkuwar jikinsu, lamarin da zai sanya su saurin kamuwa da ciwo ko tsanantar ciwon da suke fama da shi. Idan kananan yara sun yi barci a makare, to, ba za su girma yadda ya kamata ba. Tsoffafi fa? Idan ba sa barci isasshe, to, za su kara fuskantar barazanar kamuwa da wasu cututtukan da suka shafi kwakwalwa.
Ta yaya za a yi barci yadda ya kamata? Da farko ya kamata a bar wayar salula a wajen dakin kwana, bai kamata a yi wasa da wayar salula a cikin dakin kwana kafin a yi barci ba. Ya fi kyau a yi barci a lokacin daya a kullum, ba tare da sauya shi, a kokarin fito da kyakkyawar al’adar aiki da hutawa. Ban da haka kuma, wasu matasa suna son yin aiki da dare a lokacin da ba hayaniya, amma ayyuka masu wuya kan sanya su yin tunani fiye da kima, ba sa yin barci bayan sun kwanta a gado. Don haka ya fi kyau a kauce wa yin tunanin abubuwa masu sarkakiya kafin a yi barci, a samu sakin kwakwalwa. Wanke fuska, goge hakora, wanke kafafu cikin ruwa mai dumi, rufe fuska da abin kyautata fata, yin wanka, dukkansu hanyoyi ne masu dacewa na samun sakin jiki kafin a yi barci.
Har ila yau kuma, me ya sa wasu mutane ba sa jin dadin jikinsu bayan sun farka daga barci? Wannan yana da nasaba da ko katifa na da laushi ko a’a, da kuma ko matashin kai ya dace da yin barci ko a’a, yanayin kwanciya shi ma yana da muhimmanci. Idan aka kwanta da baya kan gado, to, za a samu sakin kashin baya, za a yi numfashi da kyau, amma a kan yi numfashi ta baki, ko kuma yin minshari, sannu a hankali hakan zai lalata siffofin fuskar mutane. Wasu suna son kwanciya ta gefen jiki kan gado, lamarin da zai rage yin minshari, da wadanda ke fama da cutar barci ta Apnea. (Tasallah Yuan)