Jaridar New York Times ta kasar Amurka ta ruwaito cewa, wasu fitattun kungiyoyin ‘yan kasuwa a kasar Amurka, sun bukaci gwamnatin kasar ta dawo da tattaunawar cinikayya tsakaninta da kasar Sin, da daidata karin harajin da ya samo asali daga takkaddamarsu ta cinikayya.
Jaridar ta ruwaito cewa, a cikin wata wasika da aka rubuta zuwa ga wakilin kasar Amurka a fannin cinikayya da kuma baitul malin kasar, kungiyoyin sun bukaci gwamnatin shugaba Joe Biden, ta soke harajin da take sanyawa kayayyakin kasar Sin bayan fara takkadamar cinikayya tsakanin kasashen biyu.
A cewar wasikar, saboda harajin, masana’antun kasar Amurka na fuskantar tsadar farashin sarrafa kayayyaki da samar da hidimomi a cikin gida, lamarin da ya sa sayar da wadannan kayayyaki da hidimomi zuwa ketare samun takara mai karfi a duniya.
Kungiyoyin kasuwancin sun hada da ta manoma, da ta samar da mattarar bayanai ta microchip, da ta hada magunguna da sauransu. (Fa’iza Mustapha)