Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce har kullum kasar Sin na maraba da dukkanin sassa, da su shiga a dama da su a kasuwannin kasar masu cike da moriya ga kowa.
Kalaman na sa, na zuwa ne bayan da dandalin muhawara game da cinikayya da samar da ci gaba na MDD, ya fitar da wani rahoto, dake cewa, bisa hasashe, ma’aunin GDPn kasar Sin zai karu da kaso 8.1% a bana.
Wannan rahoto, ya zo a gabar da shi ma bankin raya nahiyar Asiya, ko ADB a takaice, ya fitar da hasashen bunkasar tattalin arziki na shekarar 2021 a jiya Laraba. Cikin na sa rahoton, bankin ADB ya ce, a shekarar 2020, Sin ce ke da kaso 14.7 bisa dari, na jimillar hajojin da aka fitar sassan ketare, wanda shi ne adadi mafi yawa a duniya.
Don gane da hakan, Mr. Wang ya ce, "Hakan ya nuna yadda kasashen duniya ke kara amincewa da nasarar da kasar Sin ta cimma a fannin yaki da annoba, da kuma kwarin gwiwar su, game da kyakkyawar makomar kasar ta Sin, a fannin ci gaban tattalin arziki. (Saminu)