Cinikayyar Waje a yankin Tibet ta samu tagomashi a rabin shekarar nan

CRI2021-07-29 12:42:54

Cinikayyar Waje a yankin Tibet ta samu tagomashi a rabin shekarar nan_fororder_tibet

Alkaluman kididdiga daga hukumar kwastam ta birnin Lhasa na jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, sun nuna yadda hada hadar cinikayyar waje ta jihar Tibet dake kudu maso yammacin kasar Sin ta samu ci gaba, a rabin shekarar nan ta 2021, inda kididdiga ta nuna karuwar hakan da kaso 140 cikin shekara guda, a gabar da tattalin arzikin jihar ke ci gaba da kyautata, kuma bukatun cinikayyar waje ke kara fadada.

Wata sanarwa mai kunshe da alkaluman hukumar kwastan ta Lhasa, ta shaida karuwar hajojin da ake shigarwa da wadanda ake fitarwa daga jihar, inda darajar su ta kai kudin Sin yuan biliyan 1.98, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 304, cikin watanni 6 na farkon shekarar nan.

Yuan Jintao, jami’i ne a hukumar kwastam ta Lhasa, ya kuma ce harkokin sarrafa hajoji, da bukatun masu sayayya a Tibet na da karfi tsakanin watannin Janairu da Yuni, albarkacin managartan matakan shawo kan cutar COVID-19, yayin da kuma bukatun kasuwannin kasa da kasa ke kara fadada, kuma tattalin arzikin duniya ke farfadowa.

Jami’in ya ce jihar ta Tibet ta gudanar da hada hadar cinikayya da kasashe da yankuna 54 a duniya cikin wadannan watanni 6. Kaza lika jihar ta shigo da hajoji da suka shafi manyan fasahohi, wadanda darajar su ta kai yuan miliyan 963. Kuma mafi yawan hajojin da yankin ya fitar zuwa ketare sun shafi kayayyakin manyan masana’antun ayyukan kwadago ne, da suka hada da tufafi, da takalma. (Saminu)

—  相关新闻  —

Not Found!(404)