Babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa ta AL Ahmed Aboul-Gheit.
Yayin zantawar su a jiya Lahadi, Wang Yi ya ce Sin na goyon bayan kasashen Larabawa, game da kokarin su na bin hanya mafi dacewa ta samun bunkasuwa, tare da tunkarar batutuwan su da kan su. Ya ce Sin na kuma goyon bayan AL wajen taka rawar gani, a ayyukan wanzar da zaman lafiya na shiyyoyi, da wanzar da daidaito, tare da kawo karshen zaman dar dar a fannin siyasa da wasu kasashe mambobin kungiyar ke fuskanta.
Ministan ya kara da cewa, Sin da AL na daukar dandalin hadin gwiwar su a matsayin wata kafa, ta bunkasa alakar su a shekarun baya bayan nan. Kuma Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashen Larabawa, wajen aiwatar da sakamakon taron ministocin sassan biyu karo na 9, tare da ci gaba da hadin kai, don gina al’ummar Sin da kasashen Larabawa mai makomar bai daya.
A nasa tsokaci kuwa, Ahmed Aboul-Gheit cewa ya yi, kasashen Larabawa da Sin na da dangantaka mai karfi, kuma kungiyar AL na fatan kara karfafa dangantaka da Sin.
Mr. Gheit ya kuma godewa kasar Sin, bisa tallafin kayan yaki da cutar COVID-19 da ta samarwa kungiyar.
Ya ce AL ta gamsu da matakin adalci da Sin ke bi, game da batutuwan da suka shafi yankuna, tana kuma goyon bayan manufofin Sin na warware takaddamar dake shafar yankuna, da wuraren da ake fama da tashe tashen hankula. A hannu guda kuma, kungiyar za ta ci gaba da tattaunawa da Sin, don kaiwa ga cimma nasarar taron sassan biyu dake tafe. (Saminu)