Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana Litinin din nan cewa, dan majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai halarci taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G20 da zai gudana ta kafar bidiyo.
Ya kara da cewa, Wang Yi zai halarci taron ne bisa gayyatar takwaransa na kasar Italiya Luigi Di Maio, za kuma su tattauna batutuwa kamar cudanyar bangarori daban-daban, da tsarin tafiyar da harkokin duniya da sauran mahalarta taron.(Ibrahim)