A yau Juma’a 25 ga watan nan, babban dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron murnar cika shekaru 50, da mayarwa kasar Sin halastaccen matsayin ta a MDD. Kuma cikin jawabin sa na kaddamar da taron, Wang Yi ya ce a yanzu kasar Sin na sakawa kasashe masu tasowa, ta hanyar goyon bayan kudurorin ci gaban su.
Wang Yi ya ce a ranar 25 ga wayan Oktoba na shekarar 1971, yayin taro na 26 na babban zaman MDD, an zartas da kuduri mai lamba 2758 da gagarumin rinjaye, matakin da ya haifar da mayarwa Sin hakkokin ta a matsayin kasa daya tilo dake wakiltar al’ummar Sinawa a MDD.
Ya ce wannan muhimmin mataki ya baiwa Sinawa da yawan su ya kai kaso 1 bisa 4 na daukacin jama’ar duniya, damar tsayawa matsayin su tsakanin sauran sassan duniya.
Wang Yi ya ce tsohon shugaban kasar Sin Mao Tsedong, ya taba cewa kasashe masu tasowa ne suka mayar da Sin zauren MDD, kalaman dake nuna zurfin abotar Sin da sauran kasashe masu tasowa. Ya ce Sin ba za ta taba mantawa da wannan tarihi ba.
Cikin sama da shekaru 50 da suka gabata, Sin na nacewa manufar kare kima da moriyar kasashe masu tasowa, tana kuma magana da yawun kasashe masu tasowa karkashin manufar hadin gwiwa.
Har ila yau a baya, Sin ta sha tsayawa tare da kasashe masu tasowa. A yanzu ma, da ma nan gaba, Sin za ta ci gaba da jefa kuri’ar ta a MDD ga kasashe masu tasowa, tare da goyon bayan adalci a dukkanin harkokin kasa da kasa. (Saminu)