Ministan harkokin wajen Sin ya bayyana matsayar Sin kan rikicin Falastinawa da Isra’ila

CRI2021-05-16 17:14:05

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, a jiya Asabar ya bayyana matsayar kasar Sin game da halin da ake ciki dangane da rikicin al’ummar Falastinawa da Isra’ila a lokacin tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Pakistan Shah Mahmood Qureshi.

A ‘yan kwanakin nan, rikici tsakanin Falastinawa da Isra’ila na ci gaba da kara rincabewa, inda aka samu hasarar rayuka masu yawa, wanda hakan abin bakin ciki ne, in ji Wang Yi, a yayin da yake bayyana matsayin kasar Sin kan lamarin.

Da farko, Wang ya ce, tun asali dalilin da ya haifar da lalacewar yanayin da ake ciki shi ne tun a lokaci mai tsawo da ya shude ba a dauki matakan warware batutuwan dake shafar Falastinawa ba.

Na biyu, Wang ya ce, abin da ake bukata a halin yanzu shi ne tsakaita bude wuta da dakatar da tashin hankalin, kuma kwamitin sulhun MDD yana da alhakin neman kawo karshen barkewar tashin hankalin tun da wuri.

Na uku, Wang ya ce, hanya mafi dacewa wajen daidaita batutuwan dake shafar Falastinawa ya dogara ne kan aiwatar da yarjejejniyar kafa kasashe biyu masu ‘yancin kansu. Sin za ta jagoranci shirya mahawara kan rikicin da ya barke tsakanin Falastinawa da Isra’ila a kwamitin sulhun MDD a yau Lahadi, kuma ana fatan dukkan bangarori za su gabatar da bayani da murya guda kan wannan batu.

A nasa bangaren, Shah Mahmood Qureshi ya ce, kasar Pakistan ta goyi bayan matsayar da kasar Sin ta dauka game da tashin hankalin dake faruwa a halin yanzu tsakanin Falastinawa da Isra’ila, tare da goyon bayan warware matsalar ta hanyar kafa kasashe biyu masu zaman kansu da warware matsalolin al’ummar Falastinawa, da kuma gangamin neman warware takaddamar ta hanyar tattaunawar sulhu da cimma daidaito tsakanin bangarorin Falastinawa da Isra’ila.(Ahmad)

—  相关新闻  —

Not Found!(404)