Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce Sin za ta nace ga goyon baya da taimakon juna da hadin gwiwa da sauran kasashe, domin dakile cutar COVID-19.
Wang Yi ya bayyana haka ne yayin wani taro na musamman na ma’aiakatar harkokin wajen kasar domin gabatar da lardin Hubei ga duniya mai taken “Kwarzuwar Hubei: Ta Farfado Domin Sabbin Nasarori”.
A cewarsa, matakan lardin Hubei na yaki da annobar, misali ne na kokarin kasar Sin, wanda kuma ya bayyana ruhi da karfinta.
Ya ce a ranar 8 ga watan Afrilu aka cika shekara 1 da dage matakin kulle a Wuhan, inda ya ce a matsayinsa na wuri na farko da aka samu rahoton bullar annobar, kana wuri na farko da aka takaita yaduwar cutar, cika shekara 1 da kawo karshen kulle a birnin, abun farin ciki ne ga Sinawa, haka kuma ya ja hankalin duniya baki daya.
Har ila yau, Wang Yi ya ce, lardin Hubei da babban birninsa Wuhan, sun kasance kan gaba kuma fagen dagar yaki da annobar COVID-19, kana ba sadaukarwa ga kasar Sin kadai al’ummar yankin suka yi domin shawo kan annobar ba, har ma da ba da gagagrumar gudunmuwa ga yakin da duniya ke yi da annobar. (Fa’iza Mustapha)