A yau Alhamis kasar Sin ta harba rukunin tauraron dan adama mafi muhimmanci ga aikin binciken sararin samaniyar kasar, wannan yana daga cikin jerin muhimman ayyukan gina tashar binciken ta sararin samaniyar kasar wanda ake sa ran kammalawa zuwa karshen shekara mai zuwa.
Rukunin tauraron dan adam na Tianhe, zai kasance a matsayin muhimmin bangare na kafa tashar binciken sararin samaniya ta Tiangong, wato wuri mai matukar girma, wanda yake dauke da rukunin rokokin tauraron dan adam guda uku a yayin zamansa na gajeren lokacin, ko kuma guda biyu dogon lokacin da zai shafe.
Tashar binciken zata zamto mai siffar ‘T’ mai dauke da muhimman rukuni a cibiyar da kuma wajen gwaje gwaje a cikin kowanne. Kowane rukuni zai iya kaiwa sama da ton 20. Yayin da idan kowace tashar tana dauke da babban jirgin daukar na’urar binciken sararin samaniyar, nauyinsa zai iya kaiwa kusan ton 100.
Za a bude tashar a kasan duniyar Earth a kewayen nisan kilomita 340 zuwa kilomita 450. An tsarata ta yadda zata shafe tsawon shekaru 10, amma masana sun yi amanna cewa zata iya shafe sama da shekaru 15 ta hanyar bada kyakkyawar kulawa da yi mata gyare gyare. (Ahmad)