A jiya Laraba kasar Kenya ta dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen saman fasinja daga kasar Indiya nan da makonni biyu sakamakon karuwar annobar COVID-19 dake cigaba da ta’azzara a kasar ta nahiyar Asiya.
Sakataren hukumar lafiyar kasar, Mutahi Kagwe, ya ce an dauki matakin dakatar da sufurin jiragen saman ne bayan taron da kwamitin ayyukan gaggawa na yaki da cutar COVID-19 ya gudanar a ranar Talata bisa lura da halin da ake ciki.
Kagwe ya ce, dakatar da sufurin jiragen saman zai fara aiki ne daga tsakiyar daren ranar Asabar, ya kara da cewa, manyan jiragen saman dakon kaya za su cigaba da aikinsu tare da bin matakan kariya daga cutar a tsarin sufurin.(Ahmad)