Cibiyar likitanci ta Southwestern ta jami’ar Texas ta kasar Amurka ta kaddamar da wani rahoton nazari a kwanan baya, inda aka bayyana cewa, idan mutane wadanda suke fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar mantuwa, suna motsa jiki sosai a ko wane mako, da alamun hakan zai taimaka wajen rage saurin koma bayan kwakwalwarsu.
Mene ne cutar mantuwa? Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, “cutar mantuwa, wata nau’in cuta ce dake shafar kwakwalwa, wadda daga bisani ta kan shafi yanayin koyo da adana muhimman abubuwa. Wasu nazarce-nazarcen da aka gudanar a baya sun nuna cewa, wadanda ba su yawan motsa jiki, sun fi fuskantar matsalar saurin koma bayan kwakwalwa. Wani babban dalilin da ke haddasa wannan matsala ta mantuwa, ita ce koma bayan kwakwalwa, har ma kwayoyin kwakwalwa su ke mutuwa. Ya zuwa yanzu ba a warkar da masu fama da wannan lalura.”
Masu nazari daga Cibiyar likitanci ta Southwestern ta jami’ar Texas ta kasar Amurka sun gudanar da gwaji kan ‘yan shekaru 55 ko fiye da haka cikin 70 wadanda suke fama da matsalar rike muhimman abubuwa. An raba wadannan mutane zuwa rukunoni 2, wasu dake cikin rukuni na A suna motsa jiki sau 4 zuwa 5 a ko wane mako, inda kuma suka dauki akalla rabin awa suna motsa jiki sosai. Wasu daga rukuni na B kuma suna mike jikinsu ne kawai ma’ana ba sa cikakken motsa jiki
Sakamakon gwajin ya nuna cewa, a lokacin gwajin, kwarewarsu a fannonin rike muhimman abubuwa da warware batutuwa sun kusan yin daidai da juna. Amma hotunan da aka dauka kan kwakwalwarsu sun shaida cewa, saurin raguwar girman wani bangare dake kula da adana abubuwa da ke cikin kwakwalwar wadanda su kan motsa jiki sosai, ya ragu. Wannan bangare mai kula da adana abubuwa da ke cikin kwakwalwa ya samu koma baya ne sakamakon tsanantar matsalar karancin basira.
Masu nazarin sun yi nuni da cewa, motsa jiki sosai yana taimakawa lafiyar kwakwalwa. Ko da yake motsa jiki sosai ba iya hana raguwar girman bangaren dake kula da adana abubuwa da ke cikin kwakwalwa ba, amma yana rage saurin raguwar. Nan gaba masu nazarin za su ci gaba da nazarinsu don tabbatar da cewa, ko rage saurin raguwar girman bangaren dake kula da adana abubuwa da ke cikin kwakwalwa zai yi tasiri kan kwarewar mutane wajen koyo da adana muhimman abubuwa da kuma yadda hakan zai yi tasiri. (Tasallah Yuan)