Ma’aikatar kula da tattalin arziki da masana’antu ta Isra’ila, ta ce Isra’ilar da Morocco, sun fara tattaunawa kan hadin gwiwa a bangarori da dama dake da nasaba da tattalin arziki.
Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ce, wannan ya biyo bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar dawo da hulda tsakanin kasashen biyu da aka yi a ranar 22 ga watan nan.
Ta kara da cewa, ministan kula da tattalin arziki da cinikayya na Isra’ila Amir Peretz ya tattauna da takwaransa na Morocco Moulay Hafid Elalamy kan tsara yarjejeniyoyin hadin gwiwa a bangaren tattalin arziki da za a yi a nan gaba, wadanda za su shafi bangarorin ruwa da aikin gona da tsaron internet da masaku da tsarin kiwon lafiya na zamani da kayayyakin kiwon lafiya da sauransu.
Kasashen biyu sun amince da kafa tawagogin da za su tsara ayukan hadin gwiwa a shekarar 2021. (Fa’iza Mustapha)