Tawagar Majalisar Dinkin Duniya da take aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ko kuma CAR, ta bayyana a jiya Laraba cewa, dakarun majalisar sun yi nasarar sake kwace iko da birnin Bambari dake tsakiyar kasar, wanda ‘yan tawaye suka mamaye shi a ranar 23 ga wata.
A ranar 27 ga wata ne, za’a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin CAR. A ranar 19 ga wata ne kuma, gwamnatin kasar ta ce, tsohon shugaban kasar Francois Bozizé ya yi yunkurin juyin mulki, inda ya hada kai da wasu ‘yan bindiga da sojojin haya na kasashen waje don kaddamar da farmaki a yammacin kasar, inda suka yi kokarin kutsawa cikin babban birni Bangui. Amma jam’iyyar KNK dake karkashin jagorancin Francois Bozizé ta musunta wannan zargi.(Murtala Zhang)