Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
FAO ta dauki matakan magance farin dango a Somalia
2020-11-11 11:58:22        cri

Hukumar kula da abinci da aikin gona ta MDD FAO ta sanar da cewa, tana kara daukar matakan magance matsalar yaduwar farin dango a kasar Somalia, matsalar da ke zama babbar barazana ga abinci a kasar.

A bayanan da hukumar ta fitar game da yanayin da ake ciki kan farin dangon, FAO ta ce, ana ci gaba da samun yaduwar farin dango a shiyyar tsakiyar Somalia da gabashin kasar Habasha yayin da ake gudanar da ayyukan magance yaduwar farin.

Hukumar ta kara da cewa, ana ci gaba da daukar matakai domin kashe kananan farin dango da ba su girma ba a shiyyar arewa maso yammacin Somalia. Ta ci gaba da cewa, ba a samu sabbin rahotannin yaduwar farin dango a shiyyar arewa maso gabashin kasar ba.

A ranar 27 ga watan Oktoba, FAO ta fitar da bayanan gargadi game da yiwuwar samun kwararar farin dango a Somalia, tana mai cewa, akwai yiwuwar a wasu kwanaki masu zuwa a samu karin farin dangon a kudancin Somalia.

Ta ce, yanayin ya kasance mai hadari. Ana samun karin sabbin farin dango da aka kyankyashe su a halin yanzu sun fara bazuwa a yankunan kasashen Somalia da Habasha. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China