Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Somalia ta shiga hukumar MIGA ta bankin duniya
2020-04-01 12:05:54        cri
Somalia ta zama kasa ta 182, da ta amince da shiga hukumar bankin duniya mai rajin ba da tabbacin inshora ga harkokin zuba jari, ko MIGA a takaice. A ranar Talata ne dai mahukuntan kasar suka tabbatar da shigar kasar wannan hukuma ta MIGA, a wani mataki na samarwa kasar jari daga sassa masu zaman kan su a matakin kasa da kasa.

Mataimakin shugaban hukumar ta MIGA Hiroshi Matano, ya ce wannan mataki zai baiwa Somalia sabbin damammaki, na samun jarin waje kai tsaye, da kuma bunkasa tattalin arzikin ta a shekaru dake tafe. Matakin gwamnatin Somaliar ya biyo bayan warware sabanin ta da bankin duniya a baya bayan nan.

Tuni dai MIGA ta sanar da fara tuntubar sassa masu samar da jari, domin zubawa Somalia jarin kudade, ciki hadda masu tallafawa harkokin noma, da masu bunkasa kanana da matsakaitan masana'antu, da na hada hadar kudade, da wadanda suka shafi fasahar sadarwa da makamashi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China