Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AMISOM ta mika ginin ofishin 'yan sanda ga mahukuntan Somalia
2020-02-21 11:22:26        cri
Tawagar ayyukan wanzar da zaman lafiya a Somalia ko AMISOM a takaice, ta ce ta mika wani ginin ofishin 'yan sanda a yankin Beletweyne dake tsakiyar kasar ga mahukuntan kasar Somali, a kokarin ta na tallafawa matakan wanzar da tsaro a kasar.

Kwamishinan AMISOM mai lura da ayyukan 'yan sanda Augustine Magnus Kailie, ya bayyana ginin ofishin dake filin jirgin sama na UgasKhalif, wanda aka mika ga hukumar 'yan sanda ta jihar Hirshabelle, a matsayin cika alkawarin AMISOM, na karfafa tsaro a filin jirgin, da ma yankunan dake makwaftaka da shi.

Da yake tsokaci game da hakan, mukaddashin kwamandan rundunar 'yan sandan yankin Hiraan Ali-Duh MahadAlle, cewa ya yi "Mun yi farin ciki da bude ofishin 'yan sanda na filin jiragen saman UgasKhalif dake Beletweyne. Mun jima muna fatan samun wannan dama ta samar da karin tsaro ga filin jirgin da kewayen sa.". (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China