Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kulla yarjejeniyoyi masu yawa a bikin CIIE duk da annobar COVID-19
2020-11-10 20:49:39        cri
Mataimakin darektan hukumar shirya bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin (CIIE) Sun Chenghai, ya bayyana cewa, duk da annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar wasu sassan duniya, an kulla yarjeniyoyi masu yawa a bikin baje kolin na bana fiye da baya.

Sun Chenghai ya bayyana haka ne yayin taron manema labaran da aka shirya, Yana mai cewa, yayin da ake kammala bikin na bana a yau, an kulla yarjejeniyoyi a fannin sayen kayayyaki da hidimomi na shekara guda da darajarsu ta kai Dala biliyan 72.62, karuwar kaso 2.1 cikin 100 kan na bikin shekarar da ta gabata. Baya ga, wasu yarjejeniyoyi da aka yi niyyar kullawa da darajarsu ta kai dala biliyan 57.83 yayin bude bikin a shekarar 2018, da kuma yarjejeniyoyin da aka kulla, da darajarsu ta kai dala biliyan 71.13 a bikin baje na biyu da aka gudanar a shekarar da ta gabata. (Ibrahim Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China