Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jimillar tattalin arzikin birnin Shanghai ta kai matsayi na shida a duniya
2020-11-07 17:24:28        cri

A halin yanzu bikin CIIE wato baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga ketare karo na uku da ake gudanarwa a birnin Shanghai dake kudancin kasar Sin ya jawo hankalin al'ummun kasa da kasa, kuma alkaluman da aka fiatar yayin taron yin bayani kan birnin Shanghai da aka kira a jiya Juma'a, sun nuna cewa, kawo yanzu kwatankwacin jimillar tattalin arzikin birnin ta riga ta kai matsayi na shida a duniya, inda ya kasance wurin da ya fi jawo hankalin manyan kamfanonin kasa da kasa yayin da suke zuba jari a yankin Asiya da tekun Pasifik.

Rahoton da cibiyar nazarin harkokin raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, a shekarar 2019, jimillar GDP na birnin Shanghai ta kai kudin Sin yuan triliyan dubu 38, jimillar da ta kai matsayi na biyu dake cikin biranen kasashen Asiya, kuma ta kai matsayi na shida dake cikin biranen kasashen fadin duniya, ana iya cewa, tasirin da ya yi wa ci gaban tattalin arzikin duniya yana kara habaka.

Kawo yanzu jimillar hedkwatocin manyan kamfanonin kasa da kasa dake birnin Shanghai ta kai 758, jimillar cibiyoyin nazarin fasahohi na kasashen ketare ta kai 475, kuma kaso 25 bisa dari na manyan kamfanonin kasa da kasa 500 mafiya girma a duniya sun kafa hedkwatarsu a birnin Shanghai, har jimillar ta fi sauran birane yawa a fadin kasar Sin.

A farkon watanni tara na bana, gaba daya jimillar jarin wajen da aka zuba a birnin Shanghai ta kai dalar Amurka biliyan 15 da miliyan 515, jimillar da ta karu da kaso 6.1 bisa dari inda aka kwatanta da makamancin lokacin bara, kuma jimillar jarin wajen da aka zuba a birnin a farkon watanni tara na shekarar bara ta riga ta karu da kaso 13 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2018, duk wadannan sun nuna cewa, 'yan kasuwar kasashen waje suna cike da imani kan makomar ci gaban birnin Shanghai, har ma suna cike da imani kan makomar ci gaban kasar Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China