Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan Kasuwan Kasashe Daban Daban: Dole A Halarci Bikin CIIE
2020-11-10 19:40:23        cri

 

 

Mista Wetzetu shi ne babban darektan kamfanin hada na'urorin injuna na Wirtgen na kasar Jamus, yanzu haka ya kwashe shekaru fiye da 30 yana aiki da zama a kasar Sin. Kamfaninsa ya fara shirya aikin halartar bikin bajekolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasuwannin kasar Sin tun a karshen shekarar bara. A cewar Wetzetu, "kasuwannin kasar Sin suna da muhimmanci matuka, idan har kamfaninka na son taka wata muhimmiyar rawa a kasuwannin kasa da kasa, to, dole ka zo kasar Sin."

 

 

Shi ma kamfanin Nachi Fujitsu na kasar Japan ya halarci bikin CIIE a karo na 3. Kamfanin dake hada na'urori masu sarrafa kansu ya taba yin amfani da bukukuwan CIIE na baya wajen kulla hulda tare da hukumomi, da fitattun kamfanonin kasar Sin. A wannan karo, kamfanin yana kokarin nuna fasaharsu ta sarrafa na'urori daga wani wuri mai nisa, don dacewa da yanayin da ake ciki a duniya na kokarin tinkarar cutar COVID-19.

 

 

Ban da wannan kuma, a wata kusurwar dakin nuna na'urori masu fasahohin zamani, an kafa wata karamar rumfa mai fadin murabba'in mita 9. Amma cikin rumfar an nuna wani irin batir wanda fasaharsa ke kan gaba a duniya. Mista Gerard, shi ne ma'aikacin kamfanin da ke samar da wannan irin Batir na kasar Denmark. Ya ce ya yi da-na-sani kan yadda ba su samu rajistar halartar bikin CIIE tun da wuri ba, shi ya sa ba su samu wuri mai kyau a cikin zauren baje-koli ba.

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fada, "dole a zo kasar Sin" don samun damar raya harkar kasuwanci. Wadannan 'yan kasuwa na kasashe daban daban sun zo nan kasar Sin ne bisa imaninsu kan ci gaban tattalin arzikin kasar, da manufar kasar ta kara bude kofarta ga kasashe daban daban. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China