Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
EU ta dauki matakan ramuwar gayya a kayayyakin da Amurka ke fitarwa
2020-11-10 11:10:29        cri
Kungiyar tarayyar Turai EU ta mayar da martani kan kayayyakin da Amurka ke fitarwa ketare inda ta buga mata harajin kwastam kan kayayyakin da take fitarwa wanda darajarsa ta kai dala biliyan 4, hukumar gudanarwar EU ce ta sanar da hakan a ranar Litinin.

Valdis Dombrovskis, mataimakin shugaban hukumar gudanarwar EU ya fadawa taron manewa labarai cewa, matakin zai fara aiki ne tun daga ranar 10 ga watan Nuwamba.

A cewarsa akwai karin wasu harajin da za a sanya kan kayayyakin da Amurkar ke samarwa wanda ya hada da sassan kananan jirage sama, da kayan amfanin gona, da kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa. Ya kara da cewa, adadin zai yi daidai da harajin da Amurkar da sanya wa tarayyar Turan.

Hukumar dake sasanto ta kungiyar kasuwanci ta duniya WTO, a ranar 26 ga watan Oktoba ta amincewa EU da ta dauki matakin ramuwar gayya kan karin harajin da Amurka ta yi ba bisa ka'ida ba, inda ta amince a buga harajin kan kayayyakin jiragen sama wanda kamfanin Boeing na Amurka ke kerawa.

A watan Oktoban shekarar bara, bayan makamanciyar shawarar da WTO ta yanke sakamakon rashin cimma matsaya kan batun karin harajin kamfanin kera injinan jiragen sama na Airbus, Washington ta dauki matakin mayar da martani wanda ya shafi kayayyakin da EU ke fitawar wanda darajarsa ta kai dala biliyan 7.5, kuma harajin ya cigaba da kasancewa duk da yake hukumar gudanarwar kungiyar EU ta dauki matakan amincewa da yin biyayya ga dokokin kungiyar WTO kana ta amince da kawar da sabanin dake tsakaninta da Amurka ta kuma daidaita batun harajin a watan Yulin wannan shekara.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China