Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban wakilin EU ya ce Amurka bata da ikon gabatar da batun mayar da takunkumi kan Iran
2020-09-21 12:06:51        cri
Babban wakilin kungiyar tarayyar turai EU a harkokin kasashen waje da manufofin tsaro Josep Borrell, a ranar Lahadi ya yi watsi da sanarwar da Amurka ta fitar ta kashin kanta ta maido da takunkumin MDD kan Iran.

Borrell ya ce, kamar yadda ya sha nanatawa a lokutan baya, Amurka ta yi gaban kanta ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a shekarar 2018, a don haka bata da ikon gabatar da shirin sake kakaba takunkumi kan Iran karkashin kudirin kwamitin sulhun MDD mai lamba 2231.

Domin tabbatar da yarjejeniyar hadin gwiwar ta JCPOA, Borrell yayi alkawarin cigaba da goyon bayan kiyayewa da kuma aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar ta JCPOA daga bangaren Iran da sauran bangarorin da batun ya shafa.

Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin muhimmin ginshikin kawar da yaduwar makaman nukiliya a duniya, kana ya bukaci dukkan bangarori masu ruwa da tsaki dasu kiyaye yarjejeniyar kuma su guji daukar duk wani matakin da zai kara lalata yanayin da ake ciki a halin yanzu.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China