Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministocin EU sun bukaci Lebanon ta magance matsalolin fashewar abubuwa
2020-08-15 15:39:24        cri
Ministocin harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai EU, sun bukaci gwamnatin Lebanon ta yi kokarin shawo kan matsalolin rikicin tattalin arziki da na zamantakewa bayan mummunan hadarin da aka samu na fashewar abubuwa a kasar wanda ya daidaita babban birnin kasar Beirut a makon jiya.

A yayin wani taro ta kafar bidiyo, Josep Borrell, babban jami'in harkokin waje da al'amurran tsaro na EU, ya ce ministocin sun bukaci hukumomin kasar Lebanon da su sake gina kyakkyawar alaka da cimma yarjejeniya da asusun bada lamuni na IMF game da batun tallafin kudade.

Sannan sun bukaci a gudanar da sahihin bincike game da fashewar, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 171, da jikkata wasu da dama, kana wasu dubban mutane suka rasa gidajensu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China