Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar tsarin mulkin Kwadebuwa ta tabbatar da nasarar Alassane Ouattara a zaben shugabancin kasar
2020-11-10 09:49:56        cri
Majalisar kundin tsarin mulkin kasar Kwadebuwa a ranar Litinin ta tabbatar da sake zabar shugaban kasar mai ci Alassane Ouattara, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da kashi 94.27 bisa 100.

Shugaban majalisar kundin tsarin mulkin kasar Mamadou Kone, ya ce an tabbatar da alkaluman zaben shugaban kasar na ranar 31 ga watan Oktoba inda aka bayyana Alassane Ouattara a matsayin sabon zababben shugaban kasar ta Kwadebuwa.

A cewar hukumar zaben kasar CEI, daga cikin jimillar yawan mutanen da aka yiwa rajista 6,066,441, an tantance ingantattun kuri'u 3,269,813 da aka kada a rumfunan zabe 17,601 dake kasar, inda aka samu kusan kashi 53.90 bisa 100 na fitowar masu zabe a kasar.

A cewar Mamadou Kone, hukumarsa bata samu wani korafi daga 'yan takarar da suka fafata a zaben ba kuma babu wani rahoton game da rashin ingancin zaben da aka gabatarwa hukumar ta CEI. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China