Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cote D'ivoire tana son hadin kan da Sin karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya"
2019-05-24 13:59:41        cri

Shugaban kasar Cote D'ivoire Alassane Ouattara ya shedawa manema labarai jiya 23 ga wata cewa, kasarsa tana son kokarin shiga aikin raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" da kuma kara hadin kanta da kasar Sin karkashin wannan shawara.

Alassane Ouattara ya fadi haka yayin da ya karbi takardar nadin sabon jakadan Sin dake kasar Wan Li a fadarsa a wannan rana, ya ce, wannan shawara ita babban aiki ne dake samun karbuwa sosai daga kasashe daban-daban. Kuma kasashen biyu na samun ci gaba mai armashi ta fuskar hadin kansu, Sin kuma ta kawo babban tasiri ga kasarsa a fannin tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa da samar da ruwa da dai sauran ayyuka.

A nasa bangare kuwa, Wan Li ya ce, Sin kuma na fatan kara hadin kan da Cote D'ivoire don tabbatar da sakamakon da aka samun a gun taron koli da aka yi a Beijing na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika don ingiza tuntubar kasashen biyu a fannoni daban-daban da kawo amfani ga jama'ar kasashen biyu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China