Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jamian lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasar Cote dIvoire sun ziyarci asibitocin karbar masu cutar COVID-19 a kasar
2020-05-06 19:54:26        cri

Rahotanni daga ofishin jakadancin kasar Sin da ke Cote d'Ivoire, na cewa, a jiya Talata, ma'aikatan lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasar ta Cote d'Ivoire don samar da gudummawar jinya, sun ziyarci asibitocin karbar masu cutar Covid-19, da ma sassan da aka kebe musamman domin killace wadanda suka yi mu'amala da masu cutar, da kuma cibiyoyin gwada cutar, inda suka yi musayar ra'ayoyi tare da takwarorinsu na kasar, dangane da dabarun jinyar masu cutar da sauransu.

Tanoh Aristophane, likita ne a asibitin koyarwa na Treichville, inda aka kebe musamman domin samar da jinya ga masu cutar Covid-19, ya kuma bayyana cewa, zuwan jami'an lafiya na kasar Sin ya karfafa wa ma'aikatan lafiya na Cote d'Ivoire niyyar samun galaba a kan cutar, kuma fasahohin kasar Sin za su taimaka wa Cote d'Ivoire, wajen shawo kan cutar cikin hanzari.

Bisa goron gayyatar gwamnatin Cote d'Ivoire, ayarin jami'an lafiya na kasar Sin ya isa birnin Abijan, a ranar 30 ga watan da ya wuce. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China