Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya taya takwaransa na Guinea murnar sake zabarsa
2020-11-09 21:04:10        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya takwaransa na kasar Guinea Alpha Conde murnar sake zabensa a matsayin shugaban Jamhuriyar Guinea.

A cikin sakon taya murnar da ya aika masa, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin da Guinea aminai ne kwarai kana 'yan uwa na hakika, kawayen da suka amince da juna. Ya kuma bayyana cewa, a shirye yake ya yi aiki da shugaba Conde, wajen karfafa hadin gwiwar taimakon juna da zurfafa alakar moriyar juna wadda za ta amfani kasashen biyu da jama'arsu. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China