Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya bayyana sabbin matakan kara bude kofa daga dukkanin fannoni
2020-11-04 21:22:03        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana sabbin matakai da kasarsa za ta aiwatar a fannin bude kofa daga dukkanin fannoni. Shugaban ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa, na bude bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su Sin karo na 3 ko CIIE na birnin Shanghai.

Shugaban ya ce kasarsa, za ta bullo da jerin hajojin da za a dakatar, a fannin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa, za ta kuma fadada wasu sassan, kamar na raya tattalin arziki ta amfani da fasahohin zamani na yanar gizo, da zurfafa sauye sauye, da kirkire kirkire a fannin cinikayya da zuba jari, da sakarwa kasuwa mara, da samar da kyakkyawan yanayi.

Kaza lika a cewar shugaba Xi, Sin za ta rage jerin fasahohin da aka hana, ko aka takaita shigo da su, ta yadda hakan zai ba da damar samar da kyakkyawan yanayi na musayar fasahohin zamani tsakanin kasa da kasa.

Bugu da kari, Sin za ta ci gaba da inganta tsarin shari'ar ta, ta yadda zai dace da na kasa da kasa ta fuskar kara bude kofa, da yin komai a bude, da karfafa kariya ga ikon mallakar fasaha, da ma yadda za su samar da kariyar shari'a, da moriyar masu zuba jari na kasashen waje. Ya ce Sin a shirye take, ta sanya hannu kan yarjeniyoyin cinikayya cikin yanci masu inganci, tare da sauran kasashen duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China