Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya taya sarki Sihamoni na Cambodiya murnar cikar kasarsa shekaru 67 da samun 'yanci
2020-11-09 19:55:30        cri
Yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikawa sarki Norodom Sihamoni na kasar Cambodiya sakon taya murnar cikar kasarsa shekaru 67 da samun 'yancin kai.

A cikin sakon taya murnar, Xi Jinping ya bayyana cewa, yana dora muhimmanci matuka kan raya alakar dake tsakanin Sin da Cambodiya, kana a shirye yake ya yi aiki da sarki Norodom Sihamoni don raya dadadden abokantakar dake tsakaninsu, da kara mutunta juna, da gina al'umma mai kyakkyawar makoma tsakanin Sin da Cambodiya, ta yadda kasashen da ma al'ummominsu za su amfana. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China