Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Karbar bakuncin CIIE ya alamta burin Sin na raba damammakinta sauran duniya
2020-11-04 21:00:17        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce karbar bakuncin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE a takaice karo na 3, ya alamta matukar burin kasar Sin na raba damammakinta na kasuwa da sauran sassan duniya, tare da ba da gudummawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya.

Xi wanda ya gabatar da jawabin bude taron na bana, da aka bude da almurun yau Laraba ta kafar bidiyo, ya ce tuni aka kai ga cimma nasarar daukacin kudurorin da Sin ta ayyana, na bude kofa ga kasashen waje yayin baje kolin na CIIE da ya gabata a bara.

Shugaban na Sin ya ce tarihi ya nuna cewa, ko mai girman hadari, da bala'u ko koma baya, bil Adama na iya samun damar ci gaba. Don haka shugaba Xi ya ce manyan burikan kasashen duniya na wanzar da ci gaba a bude kuma cikin hadin gwiwa ba za su sauya ba. Daga nan sai ya bayyana bukatar hada hannu waje guda, don shawo kan hadurra da kalubale, da karfafa hadin gwiwa da tattaunawa tare, da kara bude kofa ga duniya baki daya.

Ya ce ya kamata manyan kasashen duniya su yi jagoranci bisa misali, kana kasashe masu karfin tattalin arziki su rika aiwatar da matakai bisa dacewa, kana kasashe masu tasowa su taka rawar gani, wajen yayata bude kofa da aiki tare bisa tsari. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China