Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Abdussiker Hothemudura: an tabbatar da bin addini cikin 'yanci a jihar Xinjiang
2020-11-09 12:14:03        cri

Abdussiker Hothemudura ya gama karatu a kwalejin koyar da ilmin addinin musulunci dake jihar Xinjiang, ya kuma zama mataimakin shugaban kungiyar addinin musulunci ta kasar Sin na yanzu, kana ya zama limani na masallacin Baida dake birnin Urumqi na Xinjiang har na tsawon shekaru 18.

Girmama addinai da tabbatar da bin addinai cikin 'yanci, manufa ce da kasar Sin take gudanarwa cikin dogon lokaci. An haifi Abdussiker Hothemudura a wani gidan musulmai, wanda ya san manufofin bin addini cikin 'yanci da gwamnatin ke gudanarwa. Ya ce, bin addini zabi ne na kowane mutum. Kowane mutum na iya zabar bin addini ko a'a, da kuma bin wani addini na daban. Ya ce, ba a nuna bambanci ga mutane domin bin addini a kasar Sin.

Ban da wannan kuma, an tabbatar da gudanar da harkokin addini yadda ya kamata. Bisa ka'idoji da al'adun addinin musulunci, ana iya gudanar da ayyukan karatun Alkur'ani mai tsarki, da yin addu'a, da yin sallah, da kuma yin azumi da sauransu yadda ya kamata a cikin gida idan masu bin addini ke so, ba a hana su yin su ba. Kana an tabbatar da wallafa littattafan addinin musulunci.

Abdussiker Hothemudura ya kara da cewa, an tabbatar da horar da kwararru masu bin addinin musulunci a jihar Xinjiang. A halin yanzu, akwai kwalejojin koyar da ilmin addin musulunci 10 a jihar, kana gwamnati ta taimaka musu wajen kyautata yanayin bada ilmi, da kuma horar da sabbin masu bada ilmi kimanin dubu daya a kowace shekara. Haka zalika kuma, yankin Xinjiang yana kokarin yin mu'amala tare da kasashe musulmai, da kungiyoyin musulunci, don sada zumunta da yin mu'amalar al'adu da juna. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China