2020-11-05 11:03:10 cri |
Li Xiangqian, jami'i a ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, ya ce za a kafa cibiyoyin ne a lardunan Shanghai, da Liaoning, da Zhejiang, da Anhui, da Fujian. Sauran sun hada da Shangdong, da Guangdong da Sichuan da kuma Shaanxi. An dai sanar da wannan mataki ne, gabanin bude bikin bajekolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar Sin karo na uku(CIIE) da aka bude Jiya Laraba.
A cikin shekaru uku zuwa biyar dake tafe, kasar Sin za ta kara yawan wadannan shiyoyi na gwaji ta hanyar inganta su da tsare-tsaren kirkire-kirkire, da kayayyakin aiki, da saukaka tsarin cinikayya ta yadda hakan zai kara fadada tsarin shigo da kayayyakin kasar.
Li ya ce, ma'aikatar cinikayya za ta ci gaba da aiwatar da jerin manufofi, da nufin yayata shigo da fasahohi na zamani da na'urori da hidimomi da ma kayayyaki dake da nasaba da inganta rayuwar jama'a.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China