Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karin kamfanoni sun mika bukatun neman shiga bajekolin CIIE na badi
2020-11-06 10:28:48        cri

Jami'i mai kula da aikin shirya bikin bajekolin kayayyakin da ake shigo dasu kasar Sin CIIE ya bayyana cewa, kawo yanzu karin kamfanoni da dama sun riga sun mika bukatarsu ta neman shiga bikin bajekolin na kasa da kasa na CIIE na shekara mai zuwa.

Wang Bingnan, daraktan hukumar shirya bikin bajekolin na CIIE ya ce, a yanzu haka kamfanoni 29 sun riga sun yi rejistar shiga bajekolin CIIE karo na hudu a shekarar 2021 tun a ranar farko ta bude bikin na wannan shekarar.

A cewar Wang, wanda kuma shi ne mataimakin ministan ciniki na kasar Sin, kafin bude bikin CIIE karo na uku, wasu kamfanoni kusan 100 sun riga sun yi rejista da hukumar inda suka nemi shiga bikin a shekaru uku masu zuwa a nan gaba.

Ya ce gabatar da bukatar neman shiga bikin tun da wuri, wata alama ce dake nuna karbuwar bikin na CIIE da kuma samun tabbaci game da kasuwannin kasar Sin.

Hukumar ta sanar cewa, wasu sabbin karin kamfanonin fasaha da kayayyaki da ake samarwa a duniya za a gabatar da su a kasuwannin kasar Sin domin taimakawa tattalin arzkikin duniya wajen samun farfadowa a shekara mai zuwa.

A cewar hukumar, a bikin bajekolin CIIE mai zuwa za a gabatar da wasu sabbin bangarori. Misali, a sashen na'urorin kiwon kafiya da kayayyakin kula da lafiyar za a kafa wani yankin kirkire kirkiren fasahohi, yayin da bangaren kula da lafiyar al'umma da sashen wasanni za a fadada shi sama da wanda aka ware a wannan shekarar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China