2020-10-31 17:01:30 cri |
Cikin rahoton ta na bayan bayan nan, cibiyar Africa CDC, ta ce an gudanar da gwaje-gwaje sama da miliyan 17 a nahiyar, inda sakamako ya nuna kaso 9.5 daga ciki sun kamu da cutar.
A cewarta, zuwa jiya da rana, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 1,759,794, inda adadin wadanda suka mutu ya kai 42,336.
A cewar cibiyar, kasashe membobin kungiyar AU 13 sun bada rahoton adadin wadanda suka mutu da ya zarce yawan kaso 2.7 na duniya, ciki har da Sudan da Liberia da Malawi da Zimbabwe. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China