Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Uganda za ta yi zaben shugaban kasa a ranar 14 ga watan Janairun 2021
2020-11-05 11:13:34        cri
Hukumar zaben kasar Uganda ta ayyana ranar 14 ga watan Janairun shekarar 2021 a matsayin ranar zaben shugaban kasa.

A sanarwar da hukumar zaben kasar ta fitar ta ce, 'yan takara 11 ne za su fafata a zaben, wadanda aka tantance su a ranakun Litinin da Talata, kuma za su fara gangamin yakin neman zabe ne daga ranar 19 ga watan Nuwamba zuwa 12 ga watan Janairun badi.

Hukumar zaben ta bukaci dukkan 'yan takarar da aka amince da su a zaben fidda gwani, da wakilansu, da magoya bayansu, da ma dukkan jama'a da su kiyaye ka'idoji yadda ya kamata wadanda hukumar zaben kasar ta fitar a lokacin yakin neman zaben.

Justice Simon Byabakama, shugaban hukumar zaben kasar, a ranar Talata ya bukaci 'yan takarar su dauki dukkan matakan tabbatar da ingantuwar zaben kasar ta hanyar bin matakan kariya daga annobar COVID-19.

Daga cikin 'yan takarar 11 ciki har da shugaban kasar mai ci Yoweri Museveni, wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana karagar mulkin kasar. Babban mai kalubalantar shugaba Museveni shi ne wani shahararren mawakin kasar ne Robert Kyagulanyi Ssentamu. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China