Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kara kashe fursunoni 5 cikin fursunonin da suka tsere daga wani gidan yari a Uganda
2020-09-21 10:50:48        cri
Mai magana da yawun rundunar sojan kasar Uganda Flavia Byekwaso ta bayyana cewa, an sake kashe wasu fursunoni biyar, jimilla guda 13 ke nan, a kokarin da ake na farautar fursunoni 219 da suka tsere daga wani gidan yari da aka balle a gundumar Moroto dake arewa maso gabashin kasar.

Flavia Byekwaso ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, dakarun tsaron al'umma na kasar Uganda, sun kashe fursunoni uku da suka arce daga gidan yarin Singila a ranar Laraba da rana yayin da ake farautarsu.

Ta bayyana cewa, daya daga cikin fursunonin da ya tsere dan asalin kasar Sudan ta kudu, ya mutu ne, sakamakon raunin harbin bindiga a lokacin da ake farautarsu, yayin da gungun jama'a suka kashe fursuna na biyar a Moroto.

Ta ce, har yanzu ana ci gaba da farautar fursunoni da suka fasa gidan yarin. Sai dai daga ranar Asabar da yamma zuwa wayewar garin Lahadi, sojojin sun yi nasarar kama fursuna guda. Yanzu haka dai, an kamo tare da tsare fursunoni goma da suka tsere daga gidan yarin.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China