Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata Amurka ta shawo kan matsalolin dake gabanta kafin ta ba wasu shawara
2020-06-08 10:33:55        cri

Kakakin gwamnatin kasar Uganda, Ofwono Opondo, ya bayyana cikakken goyon bayan gwamnatin kasarsa ga dokar tsaron kasar Sin ta Hong Kong, cikin wani sharhi mai taken "Amurka ta mayar da hankali kan matsalolin dake gabanta, kafin ta fara nuna yatsa ga wasu" da aka wallafa a jaridar New Vision ta kasar.

Cikin sharhin, Ofwono Opondo, ya jaddada cewa, tsaron kasa shi ne tubalin kasancewar dukkan kasashe a duniya, kuma kare tsaron kasa bisa doka, cikakken iko ne na dukkan kasashe.

Ya ce babu wata kasa, babba ko karama, mai arziki ko akasin haka, da za ta dauke idonta daga ayyukan da suka sabawa doka, wadanda ke barazana ga tsaro da kwanciyar hankali da ci gabanta.

Ya ce a Amurka, an zargi masu zanga-zanga da laifin sace-sacen da aka yi a cikin taron jama'a. Amma an bayyana masu zanga-zanga da suka yi sata da duka da fashe-fashe da kone-kone a kan titin Hong Kong da "masu rajin kwato demokuradiyya"

Ya kuma jaddada cewa, kasashen yamma ba za su yi nasara ba wajen kawo tarnaki ga dokar tsaron kasar Sin da ta shafi batutuwan Hong Kong. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China