Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan jarida: Gada Tsakanin Shugabanni da Jama'rsu
2020-11-03 17:04:41        cri

A jiya 2 ga watan Nuwamba, wato ranar da aka ware ta yaki da cin zarafin 'yan jarida ta duniya, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kara ba 'yan jarida kariya.

A sakonsa domin wannan rana, sakatare janar din ya ce idan aka kai wa 'yan jaria hari, illar na shafar dukkan al'umma. Kuma idan aka gaza kare su, to za a gamu da cikas wajen samun labarai da daukar sahihan matakai.

MDD ta ware ranar kawo karshen cin zarafin 'yan jarida ba tare da hukunta masu aikata laifi ba, da nufin kara wayar da kan jama'a kan illar rashin gurfanar da masu cin zarafin 'yan jarida da ma'aikatan kafafen yada labarai. A kiyasin da MDD ta yi, daya daga cikin masu aikata laifin 10 ne kadai ke fuskantar hukunci.

Kasancewar muhimmancin 'yan jarida saboda tasirin da suke da shi wajen bayar da labaran da suka shafi al'umma, cin zarafinsu na da mummunan tasiri, domin zai shafi kafatanin al'umma. Ana daukar 'yan jarida a matsayin gada tsakanin gwamnatoci da al'ummominsu, domin su suke taka rawa wajen isar da sakon jama'a ga gwamnati, sannan su isar da na gwamnati ga jama'a. Za a iya cewa, 'yan jarida suke tabbatar da tsare 'yancin jama'a da kara wayar musu da kai game da hakkokinsu. Abun takaicin shi ne yadda aka kasa daukarsu da daraja, inda ake ta kai musu hare-hare, sannan masu aikata laifin ke gudanar da harkokinsu hankali kwance ba tare da fuskantar hukunci ba.

Cin zarafin 'yan jarida kan zo a nau'ika daban-daban, kama daga tsoratarwa da barazana, zuwa sace su da cin zali da cin zarafi ta hanyar lalata da kisa da kazafi da sauransu. Haka kuma, mata 'yan jarida sun fi shiga cikin hadari saboda rauninsu. Baya ga haka, wasu shafaffu da mai kan kawo cikas ga gudanar da ayyukan jarida da gangan, saboda wasu muradansu na kashin kai.

Yayin da ake bin tsarin demokradiyya da tabbatar da 'yanci a duniya, ya zama wajibi a ba 'yan jarida damar gudanar da aikinsu ba tare da tsaiko ba, domin aikin ya fi amfanawa daukacin al'umma da gwamnatocinsu maimakon su kansu 'yan jaridar.

A wannan zamani da ake ciki na wayewar kai, dole ne a tabbatar da 'yancin 'yan jarida domin samun sahihan labarai da yaki da jita-jita da sanin ainihin halin da duniya ke ciki. Jazaman ne, gwamnatoci da jama'a su himmantu wajen yaki da duk wani nau'in cin zarafin 'yan jarida da kare 'yancinsu da na aikinsu da hukunta duk wanda ya yi kokarin cutar da su domin ya zama izini ga sauran mutane. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China