Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wace irin MDD duniyarmu ke bukata?
2020-09-22 21:52:24        cri

A jiya Litinin, yayin da yake ba da jawabi a yayin taron tunawa da cika shekaru 75 da kafuwar MDD, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tunasar da shugabannin kasashen daban daban da suka halarci taron, bukatar yin nazari kan cewa; shin wace irin MDD duniyar mu ke bukata? Sa'an nan bayan da aka kawo karshen cutar COVID-19, wace rawa ya kamata Majalisar ta taka?

Dangane da wadannan tambayoyi, a madadin kasar Sin, shugaba Xi ya gabatar da shawarwari guda 4, wato tabbatar da adalci a duniya, da bin dokokin kasa da kasa, da inganta hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe daban daban, da kuma daukar takamaiman matakai maimakon maganar fatar baki.

Duniyarmu na fuskantar wasu manyan sauye-sauyen yanayi, sa'an nan annobar cutar COVID-19 ta tsananta wannan yanayin da ake ciki. Ban da wannan kuma, ana ta samun ra'ayi na daukar mataki bisa radin kai, da kuma manufar kashin dankali, yayin da ake kula da al'amuran kasa da kasa.

Karkashin wannan yanayi ne, wasu kasashe, da 'yan siyasa, ke neman dora laifi ga sauran kasashe, da yanke huldar dake tsakaninsu da sauran, da kokarin ta da zaune-tsaye a duniya, da kuma wani sabon yakin cacar baka, don neman janyo rarrabuwar kawuna, da jayayya ga duniyarmu.

A wannan lokaci, ana bukatar wata MDD mai karfi. Saboda haka, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wadannan shawarwarin, don neman daidaita yanayin da muke ciki, da kare ra'ayin kasancewar bangarori masu fada a ji daban daban a duniya. Hakan ya nuna yadda yake kokarin sauke nauyin dake bisa wuyasa, a matsayinsa na shugaban wata babbar kasa, don tabbatar da zaman lafiya a duniya, da makoma mai haske ga daukacin bil Adama. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China