Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya Na Cikin Zamani
2020-06-27 16:05:17        cri

Ranar 26 ga wata, rana ce ta Kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya. Ya kamata a tuna da ranar, musamman ma a halin yanzu da ake ciki.

Yau da shekaru 75 da kafa MDD bayan kawo karshen babban yakin duniya na biyu tare da sanya hannu kan kundin tsarin majalisar, bisa manufar warware matsalolin duniya cikin hadin gwiwa, magance barkewar yake-yake, a kokarin raya wata kyakkyawar duniya.

A cikin wadannan shekaru 75 da suka gabata, bil Adama sun samu babban ci gaba a fannonin tsaro, tattalin arziki, al'adu, da ma kimiyya da fasaha. Lamarin da ya shaida cewa, manufar kundin tsarin MDD na da amfani, wadda ke taka muhimmiyar rawa ga zaman lafiya da ci gaban duniya. Ganin yadda ya kafa wani sabon salon daidaita dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, wato ra'ayin kasancewar bangarori da dama a karkashin jagorancin MDD.

Yanzu cutar COVID-19 ta bulla a duk fadin duniya, wadda ta hallaka mutane da ma lalata tattalin arziki. Kasashen duniya na tinkarar kalubalen da ba su taba fuskanta a baya ba. A yayin da ake fuskantar matsalar, babu wata kasa da ta iya samu nasara a kan cutar ita kadai ba, kasashen duniya na bukatar hadin gwiwa sosai, a kokarin samun makami mafi karfi na kawar da annobar.

Amma wani abin da ya kamata mu lura shi ne, yayin da kasa da kasa ke kokarin hada kansu don yaki da cutar COVID-19, kasar Amurka na daukar ra'ayin kashin kai a fannoni daban daban. Alal misali, a farkon bullar cutar a kasar Sin, Amurka ta ki samar da tallafi. Yayin da take fama da cutar, sai ta fara dora laifinta a kan kasar Sin, da shafa wa Sin kashin kaji, da ma siyasantar da cutar. Bugu da kari kuma, Amurka ta nuna shakku ga kwarjinin WHO, har ma ta yi barazanar janyewa daga wannan hukumar kasa da kasa daya tak da ke kokarin kiyaye kiwon lafiyar jama'ar duniya.

A bangaren kasar Sin ma, ko da yaushe tana daukar ra'ayin cewa, hadin gwiwa shi ne makami mafi amfani wajen yaki da cutar COVID-19. Ya zuwa karshen watan jiya, kasar Sin ta riga ta tura kungiyoyin ma'aikatan jinya 29 zuwa ga kasashe 27, baya ga samar da taimakon yaki da cutar ga kasashe 150 da hukumomin duniya 4. A waje daya kuma, Sin ta fitar da kayayyakin kandagarkin cutar zuwa ga kasashe fiye da 200. Kasar Sin na bin manufofin kudin tsarin MDD bisa abubuwan da take yi.

Cutar COVID-19 ta sa bil Adama sun sake fahimta cewa, yanzu muna cikin wani zamanin da makomar kasa da kasa a hade suke, ba za a iya haye wahalhalu da ma samun wata kyakkyawar makoma ba sai an kau da sabani, tare da hada kai sosai. Wannan ita ce hanyar ci gaban bil Adama, da ma babban burin ra'ayin kasancewar bangarori da dama.

Kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Sin ya fada, bai kamata a mai da kudin tsarin MDD matsayin wani littafin da aka ajiye a kantar ajiye litattafai ba, a maimakon hakan, ya kamata a yi amfani da shi wajen jagorantar abubuwan da ake yi. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ana iya samun burin bai daya na dan Adam a cikin kundin tsarin majalisar, baya ga samun abin jagora na daidaita dangantakar kasa da kasa na zamanin yau a cikinsa.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China