Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta kaddamar da bukukuwan matasa na wata guda yayin da ake fama da COVID-19
2020-11-03 09:49:46        cri
Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta kaddamar da bukukuwan matasa na tsawon wata guda, bikin da zai mayar da hankali kan kimanin kaso 75 cikin 100 na sama da mazauna shiyyar biliyan 1.2 da ake ganin 'yan kasa da shekaru 35 da haihuwa ne.

Kungiyar ta jaddada cewa, matasa su ne "Muhimmin ginshikin ajandar raya Afirka", a don haka, ci gaban matasan nahiyar yana da muhimmanci da ma tasiri ga makomar nahiyar.

Nahiyar Afirka karkashin jagorancin hukumar gudanarwar kungiyar ta AU, tana bikin matasan Afirka na tsawon wata guda duk da yaduwar annobar COVID-19, bikin da aka fara tun daga ranar 1 ga watan Nuwamba har zuwa 30 ga wata, bisa taken, "Muryar matasa, matakai, shiga a dama da su: Gina kyakkyawar Afirka".

Daga cikin abubuwan da bikin zai mayar da hankali a kai, sun hada da karfafawa matasan Afirka gwiwar daukar kansu a matsayin jigon cimma nasarar ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063.

Saboda tasirin annobar COVID-19, hukumar kungiyar AU, za ta shafe tsawon mako guda tana gudanar da bikin ta kafofin intanet, ta hanyar janyo hankalin matasa da kafofin sadarwa abokan hulda na tabbatar da cewa, sun kai ga mahalarta bikin a sassa daban-daban na nahiyar. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China