Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci a dage takunkumin tattalin arzikin da aka azawa Zimbabwe
2020-10-26 10:48:50        cri

Shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU Moussa Faki Mahamat, ya bukaci a gaggauta dage takunkumin da aka kakabawa kasar Zimbabwe.

Jami'in hukumar gudanarwar na AU ya jaddada aniyar kungiyar ta AU na cigaba da fafutukar neman dage takunkumin da aka azawa Zimbabwe cikin gaggawa ba tare da gindaya wani sharadi ba, kuma domin goyon bayan matakin da kungiyar raya yankin kudancin Afrika SADC ta dauka don tunawa da ranar 25 ga watan Oktoba na 2020, a matsayin ranar yaki da aza takunkumi na SADC, kamar yadda kungiyar mai mambobin kasashen Afrika 55 ta fitar a ranar Lahadi.

Mahamat ya kuma bayyana aniyarsa cewa, bangarori daban daban na AU za su cigaba da bada goyon baya ga yunkurin farfadowar kasar ta shiyyar kudancin Afrika.

Shugaban gudanarwar ya jaddada aniyar AU na cigaba da yin aiki tare da kungiyar SADC domin taimakawa hanyoyin kyautata shiyyar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China