Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci a dauki matakan lumana don warware yanayin dar dar a Najeriya
2020-10-27 10:46:10        cri
Wakiliyar musamman ta kungiyar AU mai lura da harkokin mata da zaman lafiya da tsaro Bineta Diop, ta yi kira ga gwamnatin Najeriya, da ta gaggauta bin hanyoyi na lumana da tattaunawa, don kawo karshen yanayin zaman dar dar da wasu yankunan kasar ke ciki.

Kaza lika jami'ar ta yi fatan ganin gwamnatin kasar ta binciki zargin da ake yi na kisan fararen hula, biyowa bayan zanga-zangar kin jinin cin zarfi da 'yan sanda ke yiwa al'umma, tare da tabbatar da ganin an hukunta duk masu hannu a aikata wannan ta'asa.

Cikin wata sanarwa da Bineta Diop ta fitar a ranar Lahadi, ta ce tana bibiyar halin da Najeriya ke ciki a baya bayan, ta kuma lura da yadda shugaban hukumar zartaswar kungiyar ta AU Moussa Faki Mahamat ke nuna damuwa da hakan, da ma kiraye kirayen da kungiyar mata mai rajin samar da jagoranci na gari ta Afirka reshen Najeriya ke yi, na a kai zuciya nesa.

A ranar Alhamis din makon da ya gabata ne dai Mr. Faki Mahamat, ya yi matukar Allah wadai da tashin hankalin da ya barke a ranar 20 ga watan nan na Oktoba, yayin zanga-zangar birnin Ikko, lamarin da ya haifar da rasa rayuka da jikkatar mutane da dama.

Bayan hakan ne kuma yanayin rashin tabbas ya karade karin wasu sassan kasar tun daga farkon makon jiya.

Mahamat ya yi kira ga 'yan siyasa, da sauran masu fada a ji dake cikin al'umma, da su kyamaci tada tarzoma, kana su martaba hakkokin bil Adama tare da kare doka da oda. Kaza lika jami'in ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki, da su koma teburin shawarwari, domin dakile kara kazantar yanayin da ake ciki, kana a warware matsalolin da suka sabbaba rikicin ta hanyar aiwatar da managartan sauye-sauye. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China