Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IOM:An ceto sama da bakin haure 370 a gabar ruwan Libya
2020-11-02 13:16:00        cri
Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya (IOM) ta sanar a ranar Asabar din da ta gabata cewa, ta yi nasarar ceto bakin haure sama da 370 a gabar ruwan kasar Libya.

Wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Twita, ta ce yayin da ma'aikatanta ke samar da taimakon gaggawa ga bakin haure da aka ceto, a hannu guda kuma tana kokarin ganin ba a mayar da kasar ta Libya zangon da bakin haure za su rika amfani da shi wajen kokarin tsallakawa zuwa kasashen Turai ba.

Hukuma IOM ta yi kiyasin cewa, a shekarar 2020 kadai, an ceto kimanin bakin haure 10,000 a gabar ruwan Libyan aka kuma mayar da su zuwa kasar, sabanin mutane 9,225 da aka ceto a shekarar 2019.

IOM ta sha nanata cewa, Libya ba wuri ne mai tsaro da bakin haure za su rika bi ba, ganin yadda al'amuran tsaro suka tabarbare a kasar.

Kasar Libya dai ta kasance wurin da bakin haure ke amfani da shi, a kokarin da tsallaka tekun Bahar Rum don shiga yankin Turai, saboda matsalar tsaro da tashin hankali da suka barke a kasar, tun bayan hambarar da ma mutuwar tsohon shugaban kasar marigayi Muammar Gaddafi a shekarar 2011.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China