Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Libya: An fara makokin rasuwar Sarkin Kuwait
2020-09-30 09:51:16        cri
Gwamnatin kasar Libya mai samun goyon bayan MDD, ta ayyana fara zaman makomi na kwanaki uku tun daga jiya Talata, saboda rasuwar sarkin masarautar Kuwait Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah. Gwamnatin Libyan ta kuma ba da umarnin sassauto da tutar kasar.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen kasar, firaminista Fayes Serraj ya gabatar da sakon ta'aziyya ga yariman masarautar ta Kuwait Sheikh Nawaf Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah, wanda tuni aka bayyana sunan sa a matsayin sabon sarkin masarautar.

Mr. Serraj ya kara da cewa, rasuwar sarki Sabah, ta haifar da rashin shugaba mai basira, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga bautawa al'ummarsa, da ma daukacin kasashen musulmi. Ya ce sarkin ya yi iya kokari wajen mayar da Labarawa tsintsiya madaurinki daya.

Domin zaman makokin sarkin wanda ya rasu a Amurka yana da shekaru 91 da haihuwa, gwamnatin Kuwait ta ayyana makokin kwanaki 40, ciki hadda ranekun hutu uku, ga ma'aikatu da cibiyoyin gwamnatin kasar, wanda aka fara tun daga jiya Talata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China