Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Libiya ya sha alwashin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta
2020-09-02 11:22:09        cri
Firaministan kasar Libiya tsagin da MDD ke marawa baya Fayez Serraj, ya sha alwashin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, tsakanin dakarun sa da na tsagin dakaru masu helkwata a gabashin kasar.

Fayez Serraj ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin ganawar sa da babban wakilin kungiyar tarayyar Turai ta EU Mr. Josep Borrell, kamar dai yadda hakan ke kunshe cikin wata sanarwar da ofishin sa ya fitar.

Gabanin hakan, Mr. Serraj da kakakin majalissar gwamnatin kasar mai helkwata a gabashin Aguila Saleh, sun fitar da wata sanarwa dake kira da a dakatar da bude wuta a dukkanin sassan kasar, a kuma sake bude filayen hakar mai, da na jiragen sama, da tashoshin jiragen ruwa. Kaza lika a gudanar da zabubbuka, tare da mayar da biranen Sirte da Jufra na tsakiyar kasar, a matsayin yankunan da aka hana ayyukan soji.

A gefe guda, Serraj ya yi kashedin cewa, duk wani mataki na kaddamar da hari kan dakarun gwamnatinsa a ciki da kewayen birnin Sirte, na iya kawo tasiri ga yarjejeniyar tsagaita bude wutar.

Libya dai ta tsunduma cikin yanayi na halin ha'ula'i ne, tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Ghaddafi a shekarar 2011, lamarin da ya budewa 'yan ci rani mafi yawa daga sassan nahiyar Afirka damar kwarara cikin kasar, a kan hanyar su ta tsallakawa sassan nahiyar Turai ta tekun Meditireniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China